IQNA

Ruftawar  wani masallaci a Najeriya tare da mutuwar mutane

14:37 - August 12, 2023
Lambar Labari: 3489631
Sakamakon ruftawar wani masallaci da ke cike da masallata a Zaria da ke arewacin Najeriya, mutane takwas ne suka mutu tare da jikkata wasu da dama.

Kamar yadda kafar yada labarai ta Sky News ta ruwaito, a jiya, Juma’a 11 ga watan Agusta, wasu masallata 8 ne suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon ruftawar wani masallaci a birnin Zariya na jihar Kaduna, dake arewacin Najeriya.

Abdullah Kwarbai  kakakin karamar hukumar Zaria ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a lokacin da daruruwan masallata ke gudanar da sallar Juma'a a babban masallacin birnin.

Ya kara da cewa: Da farko an gano gawarwaki hudu, sannan kuma jami'an ceto sun gano wasu gawarwaki  bayan kwashe tarkacen masallacin da ya ruguje.

Rushewar gine-gine a Najeriya, kasar da ta fi kowacce yawan jama'a a Afirka, yana yin sanadiyyar mutuwar mutane da dama.

 

4161890

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: rufta masallaci najeriya ceto salla
captcha